Posts

WASIKUN QAUNA

wasika don duburwarka ta nesa Ina son  kasancewa  a tare da ke na tsawan rayuwata fiye da yadda matafiyi ke buƙatar ruwa a tsakiyar sahara, fiye da yadda gangar jiki mai numfashi ke buƙatar iska, fiye da yadda tsirrai ke buƙatar hasken rana. Ina son ki tun daga babin farko na labarin rayuwata har zuwa ƙarshe. Na yi kewar rashin kasancewar ki a kusa da ni. Ki Huta Lafiya.   Duk da muna nesa da  juna  ina iya fahimtar yanayin da kike ciki na farin-ciki ko damuwa, ina iya jiyo  bugun numfashinki a cikin zuciyata, ina iya jiyo sautin murmushinki a cikin kunnuwana. Hakan na nuna ƙarfin tasirin sonki ne a cikin jikina. Ke ce mahaɗin rayuwata. Ina Son Ki. Fatana a ce nan da  watarana  mu kasance tare a sabuwar rayuwa a  matsayin mata da miji, har ya kasance mun mallaki 'ya'ya da zamu rayu tare da su cikin farin-ciki. Burina ki kasance a tare da ni har ƙarshen rayuwa domin samun tarin kulawar da na tanadar miki a gidan  aurena . Ina Son Ki.